Kudancin Kaduna: Hausa/Fulani Da Katafawa Sun Yi Zaman Sulhu

Abokan hamayya a kudancin Kaduna sun yanke shawaran kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu bayan zaman sulhun kabilar Atyap, Hausa/Fulani a ranar Asabar.

Wadanda suka halarci zaman sulhun sun yi Alla-wadai da irin kashe-kashe da asarar rayukan da akayi kuma sun yanke shawara a yafewa juna, a taimakawa hukumomin tsaro wajen damke yan tada zaune tsaye.

Ganawar da ya gudana a cibiyar taron Mariyama da Yakubu karkashin jagorancin Agwatyap, Dominic Gambo Yahaya, ya hada shugabannin bangarorin uku a wajen daya.

Cikin shawari 14 da aka yanke, an yi kira ga mazauna Atyap su daina daukan doka a hannunsu kuma su rika mika komai ga hukuma.

Takardar yace: “Wannan zaman ya amince da lamarin cewa dukkan yan Najeriya na da hakkin zama duk inda suka dama a Najeriya, har da masarautar Atyap, ba tare da wani tsoro, barazana da cin mutunci daga kowa ba.”

“Saboda haka, muna kira ga hukumomin tsaro su tabbatar mutanen da aka kora sun dawo muhallansu.”

“An bada shawara a kafa kwamitin zaman lafiya da zai hada da Hausa, Fulani da Atyap da kuma matasansu domin tattauanwa kan lamuran tsaro lokaci bayan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.”

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatinsa tana saka na’urorin CCTV a yankin kudancin Kaduna, hakan na daga cikin kokarin karfafa tsaro tare da dawo da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da yasa hannu a ranar Litinin bayan taron da yayi da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Rabaren Supo Ayokunle da sauran shugabannin CAN a Kaduna.

Kamar yadda takardar ta bayyana, tun a watan da ya gabata, gwamnatin jihar da jami’an tsaro suke aiki wurin shawo kan rikici da kashe-kashen da suka addabi jihar.

“Muna matukar bakin ciki da rashin rayuka da ke faruwa sakamakon hare-haren da ke aukuwa a yankin.

“A yayin da muke makokin mamata, yanzu abinda za mu mayar da hankali a kai shine hana ci gaban faruwar hakan. Mun mayar da hankali wurin kawo karshen matsalar da ta addabi jihar na sama da shekaru 40.” Yace

Labarai Makamanta

Leave a Reply