Ku Zama Nagari Abin Koyi – Shawarar Buhari Ga Shugabanni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su nuna jagoranci na gari abin misalaltawa, domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a wani sako da ya aika a laccar shekara-shekara ta 2021 da ake gabatarwa a gidan Arewa House da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su fifita al’ummar kasar a gaba, a duk harkokin su, kamar yadda magabatan kasar suka yi, kamar su Sir Ahmadu Bello.

Ya jaddada cewa kyakkyawan shugabanci zai samar da wata kafa ga kasar don shawo kan kalubalenta da kuma bude manyan dama ga kasar.

Related posts

Leave a Comment