Ku Yi Tattalin Cikawa Da Imani – Nasihar Obasanjo Ga ‘Yan Najeriya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi rayuwa tagari domin cikawa da imani da kuma samun damar shiga aljanna.

Obasanjo ya sanar da hakan ne a wani taron hadin kai da aka yi na wata Majami’a da ke Ogba a jihar Legas. An yi taron ne domin mika godiya ga Ubangiji a kan nasarar da aka samu wurin birne Olufunsho Salako, matar tsohon dan majalisar wakilai, Apostle Dave Salako.

Olufunsho ta mutu ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoban 2020 tana da shekaru 59 a duniya sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

A wasikar ta’aziyya da Obasanjo ya aike wa Dave, wanda ya wakilci mazabar Remo ta tarayya tsakanin 2003 da 2011, ya ce mutuwa tabbacin rashin tabbas na rayuwa ne. Tsohon shugaban kasar ya bukaci jama’a da su ji tsoron Ubangiji.

Yayin taron mika godiyar ga Ubangiji, Obasanjo wanda ya gudanar da huduba, ya samu wakilcin dansa mai suna Seun. Obasanjo ya ce aljanna tabbaci ce ga marigayiya Olufunsho saboda daga shaidar jama’a, tana son kowa kuma ta matukar kula da iyalanta.

“A duk lokacin da Kirista ya mutu, ya kwanta bacci ne. A ranar karshe, duk za su tashi kuma a yi musu hisabi. Babu shakka za a yi wa dukkan Kiristoci hisabi,” ya kara da cewa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply