Ku Yi Koyi Da Amurka Na Hana Masu Magudi Shiga Kasashen Ku – Saraki Ga Tarayyar Turai

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattijai, ya nemi kasar Burtaniya da Tarayyar Turai da su bi kasar Amurka wajan hana masu magudin zabe a Najeriya shiga kasar su.

Saraki ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a wani taron da Cibiyar Raya ‘Yancin Dan Adam ta shirya domin bikin ranar Dimokuradiyya ta Duniya ta bana.

A ranar Litinin, Amurka ta sanya takunkumin biza ga mutanen da suka dagula zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa, kimanin shekara guda bayan ta dauki irin wannan matakin a kan wadanda suka murguda zaben 2019.

Saraki ya ce irin wadannan takunkumi matakai ne da suka zama dole don yin gargadi ga makiya dimokradiyya, kuma ya kamata a fadada su ga jami’an zabe da na tsaro.

“Shawarar da Amurka ta yanke na sanya takunkumin biza ga wasu ‘yan siyasar Najeriya saboda matsayinsu na rashin mutunta zaben 2019 abin a yaba ne,” in ji shi.

“Takunkumin ya kamata ya wuce ‘yan siyasa kuma ya hada da jami’an zabe, jami’an tsaro da jami’an shari’a wadanda ke lalata dimokiradiyyarmu ta hanyar ayyukansu a lokacin da bayan zabe.”

Ya kuma yi kira da a hanzarta zartar da dokar zaben don inganta sahihancin zaben tare da kawo karshen “tsoma baki ba bisa ka’ida ba ga harkar zabe daga hukumomin tsaro”.

“Zai yiwu ace akwai wata doka da zata hana tura sojoji don aiyukan zabe.

Ya kamata mu tabbatar da bin doka a kan wannan har ma mu ci gaba da sanya wannan a cikin kundin tsarin mulkinmu, ”inji shi.

“Yana da mahimmanci kuma mu zo da karfi wajen aiwatar da abubuwan da doka ta tanada wadanda suka tanadi ladabtar da ‘yan siyasa, jami’an tsaro,’ yan kasa da jami’an zabe wadanda aka kama suna murkushe ayyukan zabe.”

Labarai Makamanta