Ku Yi Gaggawar Rufe Asusun Banki Da Zarar An Sace Wayarku – EFCC Ga ‘Yan Najeriya

A ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba, Hukumar yaki da rashawa EFCC ta shawarci yan Najeriya wadanda aka sace wa waya su garzaya bankinsu domin a toshe asusunsu saboda tsaro.

Shugaban EFCC na yankin Sokoto, Aliyu Yunusa, ne ya bada wannan shawarar yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Laraba, a birnin na Sokoto.

Aliyu Yunusa, wanda ya yi magana kan karuwar damfara masu alaka da ATM da aka sace a Sokoto, ya bayyana manyan hanyoyi biyu da ake yin irin wannan damfarar. Hanya ta farko shine, “Canja ATM” wanda ke faruwa a lokacin da kwastomomi suka tafi ATM cire kudi ko POS inda masu yaudarar za su yi yunkurin cewa za su taimakawa mutane cire kudi a ATM.

Ya ce: “Wadanda ake zargin galibi zuwa suke yi kamar za su taimaki mutane wurin cire kudi a ATM ta hakan sai su canja musu kati su basu wanda baya aiki. “Bayan sauya katin da haddace lambar sirri na katin, mai damfarar na iya cewa matsalar sabis ne sai ya mika katin da ya riga ya canja ga mai shi kuma ya yi tafiyarsa.

“Dan damfarar sai ya tafi wani ATM din daban ya cire dukkan kudin da ke asusun wanda ya damfara ko ya tura wani asusun.”

Hanya ta biyu da ake damfarar, a cewarsa, shine ‘Satar Wayar Salula’. “A wannan karon, a kan sayar da wayar da aka sace ga yan damfara wadanda za su yi amfani da USSD su gano bayanin mutum na banki. “Hakan zai taimaka musu sanin inda bankin ka ya ke, amma ga dan damfarar da bai kware ba, zai ta gwada lambar USSD na bankuna har sai ya yi nasara.

“Sannan su yi amfani da lambar USSID na banki. Su tura kudin asusun ku zuwa wani asusun daban, galibi zuwa asusun wani da suke riga suka sace katinsa kuma sun san lamban sirrinsa.”

Ya shawarci al’umma su rika kokari suna kare bayanansu na sirri musamman lambar sirri na ATM, BVN da NIN da wayoyin salularsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply