Ku Tallata Ayyukan Gwamnatina Domin ‘Yan Adawa Su Ji Kunya – Buhari

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi kira ga ministocin sa su maida hankali sosai wajen tallata ayyukan raya kasa da raya al’umma da gwamnatin sa ta samar.

Ya ce su maida hankali sosai kada su yi sanyin jiki har masu adawa da wadanda ba su fatan alheri a gwamnatin sa su rika watsa surutan da za su dusashe hasken tauraron gwamnatin sa.

A ‘yan kwanakin nan dai shugaban kasar na fuskatar soka matsananciya daga jama’a tun bayan ƙarin farashin mai da na wutar lantarki da ya yi, inda masu sukan ke bayyana hakan a matsayin rashin tausayi.

Jam’iyyar adawa ta PDP da ɗan takarar ta Atiku na kan gaba wajen sukar shugaban kasar, lamarin da wasu ke ganin sun yi dai dai wasu kuma ke ganin adawa ce ta siyasa kawai.

Farin jinin Buhari na ƙara raguwa a idanun ‘yan Najeriya, sakamakon ƙaruwar tashe tashen hankula musamman a yankin Arewacin Najeriya da kuma hauhawar farshin kayayyakin abinci a kullum.

Labarai Makamanta

Leave a Reply