Ku Nemi Makamai Domin Kare Kai Daga ‘Yan Bindiga – Shawarar Gwamnan Bauchi

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar ya bukaci mazauna yankin da aka kai wa hari kwanan nan a karamar hukumar Alkaleri da su tashi su dauki makamai su kare kansu daga ‘yan bindigar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a fadar Hakimin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri a ziyarar da ya kai kauyen Rimi, Gwana da Yalwan Duguri domin jajanta wa wadanda ‘yan fashin suka kai wa hari.

Ya ce lamarin wani “hanyar da ba za a amince da ita ba ne” wanda dole ne a dakatar da shi ko ta yaya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Gwamnan ya shawarci jama’a da su kamo “mugayen baragurbi ” tare da hada kai da ‘yan bindigar, musamman wadanda ke aiki a matsayin masu ba da labari, inda ya kara da cewa masu laifin ba za su iya yin aiki ba tare da wasu a cikinku ba.

Da yake mayar da martani, Hakimin Yelwa Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya ce mutane 20 ne aka kashe a kauyen Rimi a lokacin hare-haren kuma yunkurinsu na kaiwa Kafin Duguri ya ci tura yayin da mutanen kauyen suka tashi domin kare kauyen.

Labarai Makamanta

Leave a Reply