Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen mako, ya ce gwamnatinsa bata shirya bude iyakokin kasar ba a yanzu. Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci abunda ake shukawa a kasar.
Buhari ya fadin hakan ne da yake amsa tambayoyi a filin Jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a lokacin wani rangadi don ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a jihar Kebbi.
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan noma, Mohammed Sabo Nanono, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take ta ba manoma tallafi domin bunkasa harkar noma.
Ya bayyana cewa noman shinkafa da ake yi a jihohin Neja, Taraba, Jigawa da Kebbi kadai zai iya ciyar da kasar gaba daya inda ya dasa ayar tambaya: “toh menene na shigo da abinci alhalin za mu iya samar da shi?”
Buhari ya ba mutane tabbacin basu tallafi a lokacin noman rani da bayan shi.
Ministan ya bayyana cewa: “shugaban kasa ya turo ni domin nazo na ga irin barnar da aka samu a jihar Kebbi. Kuma na gani. Za mu rage wa ‘yan Kebbi radadi fiye da sauran jihohin.”
Ya gargadi wadanda abun ya shafa a kan kada su yanke kauna, inda ya kara da cewar gwamnati mai ci za ta farfado dasu, cewa ma’aikatarsa na hada kai da takwaranta na agaji don basu kayan tallafi.