Shugaba Buhari ya baiwa sojojin umarnin su je su kashe wadanda suka sace yaran sannan su tabbatar ko daya daga cikin yaran kada ya ji rauni.
Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa, ta ce an gano inda wadanda suka sace daliban suke kuma sojojin sama na baiwa sojojin kasa taimakon aikin kwato yaran.
Sannan kuma Shugaban kasar ya bada umarnin a tura jami’an tsaro zuwa kowace makaranta.
Matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka dai bai rasa nasaba da yadda yake fuskantar matsin lamba tun bayan sace ɗalibai sama da 600 da ‘yan Bindiga suka yi a makarantar kwana ta Kimiyya dake yankin ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta Jihar Katsina.
Harkar tsaro dai na cigaba da fuskantar barazana musanman a yankin Arewacin kasar, inda a sashin Arewa maso Gabas ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke karkashe mutane, yayin da a yankin Arewa maso yammacin ƙasar kuwa ‘yan bindiga ke kashe jama’a babu ji babu gani.