Ku Kara Hakuri Ina Sane Da Halin Kuncin Da Ku Ke Ciki – Tinubu Ga ‘Yan Najeriya

IMG 20240225 WA0030

A sakon sa na bikin ranar dimokiradiya ta bana, wadda ke nuna yadda aka kwashe shekaru 25 ana gudanar da ita ba tare da samun targade ba. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri game da halin matsin da suka samu kan su, wanda yace yana sane da shi, kuma nan gaba kadan za su dara.

Shugaban ya kuma bayyana shirin gabatar da kudirin yiwa sabuwar dokar albashi gyaran fuska domin amincewa da sabon karin da ake tattaunawa a kai.

A yayin da ya ke jawabin, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa gwamnatinsa na dab da kai karshen maganar sabon mafi ƙarancin albashi., in ji rahoton Vanguard. Ya ce idan komai ya kammala, zai mika wa majalisar tarayyar kasar domin su amince da shi wanda ya ke da yakinin zai zama mafi dacewa ga ma’aikatan.

A cewar shugaban kasar: “Ina sane da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya. Sama da shekaru ya kamata a gyara tattalin arzikin kasar saboda lalacewa da rashin makoma.

“Tun bayan hawan mu mulki, mun aiwatar da sauye sauye wadanda suka zama tubali ga dorewar tattalin arzikin kasa

“Ko a lokacin da ‘yan kwadago suka shiga yajin aiki kan mafi ƙarancin albashi, ba mu takura masu ba, mun kyale su saboda ‘yancin su ne, saboda muna da yakinin yin adalci a gare su.”

Alakar dimokuraɗiyya da tattalin arziki Shugaban kasar ya ce da ace Najeriya na karkashin ‘yan mulkin mallaka, to ba makawa ‘yan ƙwadago ba za su samu fuskar yin yajin aikin ba.

Ya yi nuni da cewa manufar dimokuraɗiyya a kullum shi ne mutunta ‘yancin kowa, amma ba hakan ne zai sa a sauka daga turbad kundin tsarin mulkin kasar ba.

Tinubu ya sha alwashin farfaɗo da tattalin arziki da kuma gabatar da tsare tsare ta yadda za a gina Najeriya ba tare da an kuntatawa wani dan kasar ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply