Ku Harbe Duk Dan Dabar Da Ya Shiga Hannu – Umarnin Gwamnan Neja Ga Jami’an Tsaro

IMG 20240323 WA0041

Gwmnan jihar Neja, Umaru Bago, ya kafa dokar ta-baci saboda tabarbarewar tsaro a jihar, biyo bayan barkewar faɗace-faɗacen ƴan daba a babban birnin jihar, Minna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin bawan Sallah da tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu ya shirya a gonarsa da ke Minna.

Bago ya kara da cewa, ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wani dan daba da aka samu yana barazana ga zaman lafiya a jihar.

Umarnin na gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ayyukan yan daba suka sake dawowa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a daren Juma’a a Minna.

Bago, wanda ya danganta sake barkewar rikicin da ayyukan masu hakar ma’adanai a babban birnin jihar, ya ce ya bayar da umarnin rufe dukkan wuraren hakar ma’adanai.

“Na ayyana dokar ta-baci tare da umarnin harbi kan duk wani dan daba da aka gani a cikin babban birni da kuma cikin jihar.

“Ba mu da hakuri kan rashin tsaro da ‘yan daba. Mun kuma rufe wuraren da masu aikin hakar ma’adanai ke haddasa wannan barna a jihar.

“Duk wanda aka samu a wurin za a harbe shi har lahira. Wadanda ke daukar nauyin su ma za a yi musu hukunci mai tsauri,” in ji Bago

Labarai Makamanta

Leave a Reply