Ku Guji Karɓar Bashi Domin Ayyuka – Sunusi Ga Gwamnatoci

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnatoci su daina karban bashi domin aiwatar da ayyuka.

Hakazalika ya bayyana cewa rashin neman wata hanyar kudin shiga sabanin man fetur tsawon shekaru 60 yanzu ya haifar da halin talaucin da ake ciki yau.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce maimakon karban bashi, kamata yayi gwamnatoci su zuba kudi wajen gina mutane da kuma manufar janyo hankalin masu sanya hannun jari.

Ya bada wannan shawara ne a taron sanya hannun jarin da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya ranar Talata.
“Yayinda kowa ke zuwa wajen gwamnatin tarayya neman mafita, gaskiyar magana itace gwamnatin tarayya bata wani rawan takawa a tattalin arzikin kasa.”

Tsohon Sarkin ya tunatarwa da jama’a yadda tattalin arzikin Najeriya ya kasance kafin samuwar arzikin man fetur.
Ya bayyana cewa gabanin samuwar man fetur, an gina tattalin arzikin Najeriya ne kan yadda ba zata girgiza ba idan an samu matsala a kasuwar duniya.

A kan dauke hankali daga arzikin mai, ya kwatanta Najeriya da kasar Malaysiya, wacce ta cigaba daga fitar da kananan kayayyaki zuwa kere-keren abubuwansu cikin shekaru 30 daga 1970 zuwa 2000.

Labarai Makamanta

Leave a Reply