Ku Fara Duban Watan Dhul-Hajji Yau Talata – Sarkin Musulmi

Shugaban majalisar koli kan gudanar da harkokin addinin Musulunci, kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, a ranar Litinin, ya bukaci Musulmi da su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1441 bayan Hijira, a yay Talata, 21 ga watan Yuli.

Talata, 21 ga watan Yuli 2020, da tayi dai dai da 29 ga watan Dhul Qadah 1441, ita ce ranar da za a fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah 1441 bayan Hijira.” Ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun shugaban kwamitin mashawarta kan harkokin addini na majalisar, Farfesa Sambo Junaidu.

Ya bukaci Musulmi da su bada rahoton ganin watan ga masu rike da sarautun gargajiya mafi kusa da su domin isar da sakon ga majalisar.

Ya roki Allah S.W.A da ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da harkokin addinin Musulunci.
Idan ba a manta ba, a ranar 19 ga watan Mayu, 2020, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa a Masallatan Juma’a za’a gudanar da sallar Idi a bana a jahar Sakkwato da kewaye.

Gidan rediyon muryar Amurka, VOA ya ruwaito hakan na nufin Musulmai za su gudanar da sallar Idi ba kamar yadda suka saba yi a manyan filaye ba, saboda annobar Coronavirus.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin ganawa da wasu shuwagabannin al’ummar jahar Sakkwato da suka kai masa ziyara dangane da batun sallar Idin bana. Sarkin ya shaida ma wakilan cewa ba a dauki wannan mataki don hana jama’a sallar Idi ba, illa an yi ne don kare lafiyarsu, don haka ya nemi jama’a su yi biyayya ga wannan tsarin.

Bugu da kari, Sarkin ya bayyana cewa ba ma jahar Sakkwato kadai ba, jahohi da dama ma haka zasu dabbaka tsarin gudanar da sallar Idi a Masallatan Juma’a. Daga karshe kuma ya nemi shuwagabannin gwamnatoci a matakai daban daban da su cigaba da kokarin da suke yi don ganin an ga bayan annobar cutar Coronavirus.

Labarai Makamanta

Leave a Reply