Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ku Fara Duba Jinjirin Watan Al-Muharram Yau- Sarkin Musulmi

Majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi da ke Sokoto, ta buƙaci jama’ar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Al- Muharram a yau 29 ga watan Dhul-Hajji 1441 wadda ta yi daidai da 19 ga watan Agustan shekara ta 2020.

A cikin wata sanarwa da fadar mai alfarma Sarkin Musulmin ta fitar kuma aka rarraba ta ga manema labarai, an bukaci musulmi da su sanar da ganin jinjirin watan ga hakiman yankunan su, su kuma su sanar da Sarakuna sannan a sanar da fadar Sarkin Musulmi domin sanar da jama’a baki ɗaya.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bukaci musulmi da su dage wajen sanya ƙasa cikin addu’o’i domin fita daga halin masifu da iftila’in da kasar ke fama da su, sannan su sanya shugabanni cikin addu’o’i domin kai ƙasar ga tudun mun tsira.

Idan an ga watan a wannan rana ta Laraba zai zamana gobe Alhamis 20 ga watan Agusta zata zama 01 ga watan Al-Muharram na sabuwar shekarar musulunci 1442 kenan. Idan ba’a samu ganin wata ba Watan Dhul-Hajji zai cika kwanaki 30 kenan inda ranar Juma’a za ta kasance 01 ga watan Al-Muharram.

Exit mobile version