Ku Dage Ga Koyon Sana’o’i Ba Jiran Aikin Gwamnati Ba – Pantami Ga Matasa

Ministan sadarwa da fasahar zamani, Dr Isah Ali Pantami, ya bayyana cewa dole ne matasan Najeriya su maida hankali wajen koyon sana’a kuma su daina dogora da shaidan kamalla karatu zalla.

Kamar yadda ya bayyana, ‘yan Najeriya sunfi maida hankali ga samun shaida ta karatu fiye da koyon sana’o’i, ya kuma kara da cewa akwai sana’o’i da dama a kasar nan sai dai kuma rashin maida hankali a koyi sana’o’in ya sanya ba a cike guraben ba.

“Wasu lokutan idan kaje kaddamar da wani aikin, duk wanda ka kaiwa ziyara zai dauko maka tulin takurdun neman aiki”.

A duk jihar dana kai ziyara nakan dawo da takurdun neman aiki fiye da 200; wannan abun dubawa ne kwarai. Kasashe da suka ci gaba, matasansu basa son yin aiki a karkashin gwamnati sai dai aikin sa kai.

Idan aka samu horon sana’a ko daga muhallinmu zamu samu damar rage zaman banza, a bangaren mu kuma muna iya bakin kokarin mu wajen ganin mun kawo cigaba a fannin kirkira da koyar da sana’o’i.

Pantami ya bayyana haka ranar Juma’a, a wajen kaddamar da cibiyar kimiyya da fasaha a jami’ar jihar Gombe, wadda hukumar kula da cigaban kimiyya da fasaha ta kasa (NITDA) ta gina.

Ministan ya ce, “a kasashen da suka cigaba akan bawa masu shaidar karatu kaso mafi kankanta a wajen rabon aiki yayin da masu kirkire-kirkire da sana’o’i ke samun kaso mafi rinjaye.

“Shaidar takarda kamata yayi ace abune da yake tabbatar da cewa kana da fasahar kirkira ko shaidar ka kware a wata sana’a. Fasaha itace take aikin bawai shaidar takarda ba”.

A Najeriya, matsalar da muke fama da ita kenan. Ina ta kokarin ganin na haɗa kai da ‘yan uwana na majalisar zartarwar fadar shugaban kasa wajen ganin mun haɗa hannu don tabbatar da cewa ana koyon sana’o’i, ya kamata mu rage dogaro da takarda mu kuma maida hankali wajen kirkira da sana’o’i.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply