Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a ranar Asabar ya bukaci sojojin Opertion Sahel Sanity su ragargaji ‘yan bindiga da sauran miyagu ba tare da tausayi ko sassauci ba.
Ya ce rundunar sojojin ba za ta bawa masu aikata laifuka damar su numfasa ba ko kadan za ta yi musu kisa irin na gilla domin kawo karshen su gaba daya.
Buratai ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina a yayin da ya kai ziyarar duba yadda aikin rundunar Operation Sahel Sanity da aka kaddamar a Arewa maso Yamma ke tafiya.
Ya kara da cewa rundunar soji tana da karfin da za ta iya magance ‘yan bindigar da kuma dawo da doka da oda a yankin arewa maso yamma da sauran sassan Najeriya baki daya. Ya yi kira ga mutane su daina bawa masu laifi mafaka domin wata rana za su juya musu baya.
“Miyagun da ke aikata laifuka suna cikin al’ummar da ke neman kariya kuma suna da Ƙannai, Yayye da sauran dangi domin ba daga sama suka fado ba.
“Da zarar mutane sun daina boye masu laifi, za mu samu damar kawar da laifuka cikin gaggawa a garuruwan mu. “Duk da haka, muna da sabbin na’urorin zamani na tattara bayannan sirri kuma dai mutane suna kara bada hadin kai. “Miyagun suna nan suna yawo cikin gari kuma idan har ana son samar da tsaro a garuruwan mu, sai an tona asirin su,” in ji shi.