Kuɗaɗen Tsaro: Mun Ba Masari Mako 2 Ya Sauka Daga Mulki – Matasan Arewa

Ƙungiyar cigaban matasan yankin arewacin Najeriya jihohi 19 har da Abuja, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Alhaji Imrana Nas, ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Masari da ta gaggauta kare kan ta daga zargin da Dr Mahadi ya yi mata ko su gaggauta sauka daga karagar mulki.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ƙungiyar Alhaji Imrana Nas a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna dangane da sama da fadi da ake zargin Masari da muƙarrabanshi sun yi da kuɗaɗen tsaron jihar.

Matasan na Arewa sun ƙara da cewar taron manema labarai da Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya kira yana ƙaryata maganar Dr Mahadi wannan soki burutsu ne, domin dukkanin maganganun nashi kame kame ne, ko kaɗan ya gaza kare gwamnatin Jihar daga zargin da aka yi mata, domin shi Dr Mahadi ya bayyana hujjoji dalla dalla da alkalluman lissafin abin da ya faru, saboda haka muddin gwamnatin Jihar Katsina na inkari akan haka, dole ne ta bijiro da gamsassun hujjoji da zasu shafe na Mahadi.

Imrana Nas wanda shima ɗan asalin Jihar Katsina ne, ya nuna matuƙar takaici da alhinin shi dangane da cin amanar da gwamnatin Jihar ta yi wa talakawa da maƙudan kuɗaɗen tsaron da aka turo mata, inda ya bayyana cewar kungiyar Matasan Arewan ta bada wa’adin mako biyu ga gwamnatin Jihar ta kare kanta kariya ta haƙiƙa ko kuma su gaggauta sauka daga karagar mulki su nemi gafarar Katsinawa na mummunan zaluncin da suka yi musu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply