Kotun koli ta sanar da cewa Olukayode Ariwoola zai yi ritaya a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya a ranar 22 ga watan Agusta.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Festus Akande mai magana da yawun kotun koli ya ce za a gudanar da zaman kotun na ban kwana domin girmamawa ga alkalin alkalan wanda ke cika shekaru 70 na ritaya.
Akande ya kuma ce kotun kolin ta fara hutun ta na shekara a ranar 22 ga watan Yuli inda za ta dawo a ranar 23 ga watan Satumba na 2024.
“Shekarar aiki ta 2023/2024 ta zo karshe a ranar Juma’a 19 ga watan Yuli na 2024″, inji sanarwar.
” Kotu ta fara hutu a ranar Litinin 22 ga watan Yuli na 2024 kuma za ta dawo a ranar 23 ga watan Satumba na 2024.”
A ranar 12 ga watan Oktoba na 2022 ne dai tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alkalin alkalan Najeriya wata 4 bayan ajiye aikin da Ibrahim Muhammad ya yi.