Babbar mai gurfanarwa a kotun duniya mai binciken manyan laifuka ICC, ta bayyana cewa kotun a shirye ta ke domin fara binciken hukumomin tsaron Nijeriya a kan laifukan da suka shafi ”cin zarafin al’umma” da saba ka’idojin yaki, da sauran manyan laifuka da ake zargin su da aikatawa.
Kotun Duniya ta ICC kotu ce ta kasa da kasa da ke tuhumar manyan laifukan ta’addanci da cin zarafin jama’a. Helkwatarta ta na kasar Switzerland.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zarge-zarge suka yi yawa a kan cewa jami’an hukumomin tsaro a yankin arewa maso gabas da sauran sassan Nijeriya suna cin zarafin fararen hula da sauran abubuwa na assha.
An ruwaito cewa takardar da ta kunshi bayanin ba ta bayar da takamaiman zargi ko zarge-zargen da kotun za ta bincika ba, sai dai, ta bayyana cewa “akwai isassun hujjojin da ICC za ta gudanar da bincike akansu.
Ofishin mai gurfanarwar ya ce ICC ta gudanar da bincike a gurguje tare da nazarin wasu zarge-zarge da suka shafi kisan dumbin jama’a, cin zarafi da keta haddinsu tare da kyararsu.
“Muna son jin amsoshin tambayoyinmu uku daga bakin Buhari Fatou Bensouda, mai gurfanarwa a kotun ICC, ta ce “akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa jami’an hukumomin tsaron Nigeria (NSF) sun aikata wadannan laifukan cin zarafin jama’a da laifukan da suka shafi yaki
“Laifukan sun hada da kisa, azabtarwa, cin zarafin mata, kai hari a kan daidaiku da gungun fararen hula, daukan yara ‘yan kasa da shekaru 15 aiki da sauransu.” Ta kara da cewa “akwai kwararan hujjoji da ofishina keda su, hujjoji na zahiri da za’a iya kimantasu.
Ofishina zai samar da karin bayanai a taron shekara da zamu yi nan bada dadewa ba.”