Kotun ?aukaka ?ara a ta ?asa ta jingine hukuncin da ta yanke game da bu?atar da gwamnatin tarayyar kasar ta gabatar, na neman kada a yi gaggawar sakin jagoran yan aware na IPOB Nnamdi Kanu.
Mai sharia Haruna Tsamani wanda ya jagoranci zaman a Abuja a ranar Litinin, ya sanar da cewa za a bayyana wani hukuncin nan gaba ga duka bangarorin biyu da zarar sun gama kintsawa.
Gwamnatin tarayya ce ta shigar bukatar jinkirta aiwatar da hukuncin da kotun ?aukaka ?arar ta yanke a ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, wadda ta yi watsi da wasu tuhume-tuhume bakwai da ake yi wa Kanun.
Ciki har da yadda aka du?un?uno Kanu aka kawo shi Najeriya daga Kenya ya saba wa dokar ?asashen duniya, kai tsaye kotun ta yi umarnin a wanke Kanu daga zargin taaddanci.
To sai dai gwamnatin tarayyar ta hannun lauyanta David Kaswe ta nuna jayayya da hukuncin tana mai cewa tun da farko Kanu ya sa?a wa ?aidar beli a 2017.
Ya ?ara da cewa suna neman a ci gaba da rike Kanu ne domin tabbatar da zaman lafiyar yankin Kudu maso Gabas, da kuma Najeriya baki daya.