Kotun ɗaukaka ƙara a ta ƙasa ta jingine hukuncin da ta yanke game da buƙatar da gwamnatin tarayyar kasar ta gabatar, na neman kada a yi gaggawar sakin jagoran ‘yan aware na IPOB Nnamdi Kanu.
Mai shari’a Haruna Tsamani wanda ya jagoranci zaman a Abuja a ranar Litinin, ya sanar da cewa za a bayyana wani hukuncin nan gaba ga duka bangarorin biyu da zarar sun gama kintsawa.
Gwamnatin tarayya ce ta shigar bukatar jinkirta aiwatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke a ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, wadda ta yi watsi da wasu tuhume-tuhume bakwai da ake yi wa Kanun.
Ciki har da yadda aka duƙunƙuno Kanu aka kawo shi Najeriya daga Kenya ya saba wa dokar ƙasashen duniya, kai tsaye kotun ta yi umarnin a wanke Kanu daga zargin ta’addanci.
To sai dai gwamnatin tarayyar ta hannun lauyanta David Kaswe ta nuna jayayya da hukuncin tana mai cewa tun da farko Kanu ya saɓa wa ƙa’idar beli a 2017.
Ya ƙara da cewa suna neman a ci gaba da rike Kanu ne domin tabbatar da zaman lafiyar yankin Kudu maso Gabas, da kuma Najeriya baki daya.