Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kotun ?aukaka ?ara Ta Wanke Nnamdi Kanu Daga Dukkanin Tuhuma

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar K?otun daukaka ?ara ta kori ?arar gwamnati tarayya a kan jagoran ?ungiyar ?an aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

T?awagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.

H?ukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.

A?lkalan sun ce an dawo da shi Najeriya ne ba bisa ?a’ida ba.

S?annan sun ce gwamnatin tarayya ta gaza fa?ar wajen da ta kama Kanu duk da manya-manyan zarge-zargen da take yi masa.

K?otu ta ?ara da cewa shirun da gwamnatin ta yi na nuna cewa ta yarda da abin da Kanu ya ce cewa sato shi aka yi aka dawo da shi Najeriya da ?arfi.

K?otun ta ce tsare Kanu da yi masa shari’a a kowace kotu karya doka ne tun da ba bisa ?a’ida aka mayar da shi Najeriya ba.

Exit mobile version