Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke tsohon sakataren gwamnatin tarayya Mista Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga zargin wata bada?ala ta ku?i naira miliyan 544.
Hukumar ya?i da cin hanci da yi wa tattalin arzi?in ?asa zagon ?asa ta Najeriya, EFCC ce ta gurfanar da mutanen, tana zargin su da almundahana kan wata kwangilar cire ciyawa, wadda ku?inta ya kai naira miliyan 544.
Mai shariaa Charles Agbaza ya ce babu wani abu da zai nuna cewa Babachir yana da laifi a cikin bayanan da shaidu 11 da EFCC ta gabatar suka bayar.
Haka nan kotun ta ce EFCC ta kasa tabbatar da cewa Babachir jamii ne a shirin ofishin shugaban ?asa na tallafa wa arewa maso gabas, wanda ya bayar da kwangilar aikin.
A kan haka ne kotun ta ce ta wanke dukkanin mutane 10 da ake tuhuma a ?arar.