Kotu Ta Umarci INEC Ta Cigaba Da Yi Wa ‘Yan Najeriya Rijistar Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta hanzarta cigaba da yi wa jama’a rijistar katin zabe har sai kwanaki 90 sun rage na zaben 2023 mai zuwa.

A yayin yanke hukunci, Mai shari’a Ekwo ya kara da umartar INEC da ta tabbatar da cewa duk wani ‘dan Najeriya da ya kai shekarun yin zabe an bashi damar yin katin zabe. Yace hakkin hukumar zaben ne ta samar da abinda ya dace yayin biyayya ga dokokin Najeriya.

Wata Amanar Salmat da wasu mutum uku ne suka maka INEC a gaban kotu inda suka ce hukumar bata isa ta dakatar da yin rijistar katin zabe ba, ba tare da ta duba tanadin kundin tsarin mulki ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply