Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja a ranar Alhamis ta sanya ranar 27 ga watan Satumba domin sauraron karar da wata kungiyar ta shigar gabanta inda take kalubalantar matsayin kasancewar tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar cikakken dan kasa.
Kungiyar ta shigar da karar tun 2019 inda take kalubalantar cancantar tsayawa takarar shugabancin kasa na Alhaji Atiku Abubakar. A lokacin da aka karanto karar, lauyan masu shigar da karar Akinola Oladimeji ya fada wa kotun cewa bai shirya wa tunkarar karar ba tukuna.
Lauyan ya fada wa kotun cewa sai a ranar Laraba ne aka sanar da shi cewa za a saurari karar a ranar Alhamis tun bayan da a farko aka sanar masa cewa an dage zaman zuwa ranar 20 ga watan Satumba.
Alkalin, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya nemi sanin cewa ko an sanar wa dukkanin bangarorin biyu kan zaman da za a yi a yau daga bakin rajistara na kotun inda ya ya ce eh an sanar. Daga nan sai alkalin ya nuna bacin ransa kan yadda ya ce ya saka ranar zaman wanda daga karshe ya zama abin ce-ce-ku-ce.
Sai dai daga bisani ya dage zaman zuwa ranar 27 ga watan Satumba tare da jan kunnen masu karar cewa wannan ne karo na karshe da za a dage sauraron karar.