Kotu Ta Sanya Ranar Saurarar Bukatar Miƙa Kyari Amurka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Kotun tarayya dake zamanta a birnin ta zaɓi ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara tafka mahawara kan bukatar gwamnatin tarayya na miƙa Abba Kyari zuwa Amurka.

An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ofishin Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ta shigar da bukatar gaban Kotu, ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022. Karar wacce aka raɗa wa, “Neman sahalewar miƙa Abba Kyari ga ƙasar Amurka,” na ɗauke da kwanan wata dai-dai da ranar da aka shigar da ita 2 ga watan Maris.

Haka nan kuma, Antoni Janar shi ne wanda ya shigar da ƙarar, yayin da mataimakin kwamishinan yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ne ake neman umarnin Kotun a kansa.

An shigar da bukatar ne karkashin dokar miƙa dan ƙasa a wani bangare na amincewar da gwamnatin Najeriya ta yi wa bukatar Amurka na miƙa mata Abba Kyari.

Gwamnati ta tura bukatar ne kai tsaye ga shugaban Alkalai, tare da masa bayanin cewa bukatar ta fito ne daga ofishin diflimasiyya na ofishin jakadancin Amurka a Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply