Babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Sabon Gari karkashin jagorancin mai shari’a Kabir Dabo ta fara sauraron karar da aka shigar na kallubalantar nadin da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi wa Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau.
An nada Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 ne bayan rasuwar tsohon sarki Alhaji Shehu Idris.
Tunda farko an ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar sarautar ta Zazzau, Iyan Zazzau, Bashar Aminu ya shigar da kara kotu yana ƙalubalantar rashin sahihancin rawanin Sabon Sarkin.
Bashir Aminu na daya daga cikin mutane hudu da masu zaben sarki suka mika sunayensu ga gwamnan don zaben daya daga cikinsu da zai nada sarki, kuma shine ya samu kuri’u mafi rinjaye a kuri’ar da masu zaben sarkin suka kada.
Amma gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da zaben na su ta bada umurnin a sake sabon zabe. Jerin sunayen na biyu da aka gabatarwa gwamnatin ya kunshi sunan Bamalli wadda daga bisani aka zabe shi ya zama sarki.
Iyan Zazzau Bashar Aminu wanda ɗa ne ga marigayi Sarkin Zazzau Aminu dags gidan sarautar Katsinawa, a cikin karar da ya shigar ya ce ba ayi adalci ko kaɗan ba wurin zaben.
Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba, na wannan shekarar.