Kotu Ta Bada Umarnin Kama Mawa?i Rarara

Kotun Shari’ar Musulunci, da ke zaune a Kano, ta ba da umarnin a kama shahararren mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara, a ranar Talata.

Alkalin da ke sauraren karar, Khadi Ibrahim Sarki Yola, ya ba da umarnin ne bayan mawakin ya ki bayyana a gaban kotun don kare zargin da aka gabatar a kansa.

Kotun a baya ta gayyaci shahararren mawakin da ya bayyana a gabanta a ranar 22 ga Disamba, 2020, kan wata kara da ta zarge shi da boye wata matar aure.

Mijin matar ya shigar da kara a gaban kotun Shari’a yana neman ha??in sa.

Mai shigar da karar ya yi ikirarin cewa Rarara ya jefa matar aure a cikin bidiyon wakarsa mai suna ‘Jihata, Jihata ce’, daga nan ne har yanzu ba a san inda take ba.

Related posts

Leave a Comment