Kotu Ta Bada Umarnin A Yashe Asusun Ajiyar Yari

Wata babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden asusun ajiya da ke Bankuna na tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ba tare da wani jinkiri ko ?ata lokaci ba.

Kudaden sun hada da wadanda ke bankunan Zenith da Polaris da sauran Bankuna da Gwamnan ke ajiya a fa?in Najeriya kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa kudaden da ke Bankin Polaris sun kai dala hamsin da shida. Akwai Naira miliyan 12.9, Naira miliyan 11.2, dala 30,309.99, Naira 217,388.04, dala 311,872.5 wadanda aka adana a bankin Zenith duk da sunan tsohon gwamnan da kamfanoninsa.

Kamar yadda alkalin kotun ya yanke, ya ce babu dalilin da zai sa hukumar ICPC wacce ta shigar da karar ta kasa kwace kudaden bisa ga tarin gamsassun hujjoji da ta gabatar.

Idan za mu tuna, hukumar ICPC tana zargin tsohon gwamna Abdulaziz Yari da samun makuden kudaden ta haramtacciyar hanya, a lokacin da yake gwamna a Jihar Zamfara.

Related posts

Leave a Comment