Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatar kasashen duniya su hada kai tare wajen tunkarar cutar COVID-19 kamar sauran kalubalen da suka jiɓinci rashin tsaro da ke addabar duniya.
Da yake jawabi a wajen taron karbar takardun wasikar amincewa da sabbin jakadun Masar, Saudi Arabia da Argentina a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana cewa:
“Muna da kalubale iri daya da ke tasiri sosai ga kasashenmu, wadanda suka hada da ta’addanci, tayar da kayar baya, canjin yanayi, fashewar jama’a, safarar mutane, rashawa, talauci, da kuma yaduwar kananan makamai.
“A saman wadannan duka, zango na biyu na annobar COVID-19 ya zo da iri daban-daban da ke haifar da karin kalubale ga bullowar farko.
Shugaba Buhari ya kuma nuna matukar farin cikinsa ga hadin kan da Najeriya da sauran kasashen uku suka samu a wasu fannoni.
“Duk kasashe ukun da aka wakilta a nan suna da kyakkyawar dangantakar bangarori tare da mu.
Jakadun, wadanda suka gabatar da wasikun amincewarsu, su ne: Mista Ihab Moustafa Awad Moustafa daga Jamhuriyar Larabawa ta Masar, Mista Faisal Ebraheem Alajrafi Alghamdi daga Masarautar Saudiyya, da Mista Alejandro Miguel Francisco Herrero daga Jamhuriyar Argentina.
Shugaban ya nanata wa Jakadun shirin na Najeriya “don yin aiki tare da ku baki daya don samun zaman lafiya a duniya, wadatar abinci da muhalli mai dorewa.”
“A madadin Gwamnati da jama’ar Najeriya, ina kira gare ku, a yayin gudanar da ayyukanku a Najeriya, da ku dora kan nasarorin magabata da kuma inganta dangantakar ‘yan uwantaka tsakanin kasashenmu.
Da yake magana a madadin sauran jakadun Ihab Moustafa ya nuna godiya ga shugaban bisa karbar su da kuma karbar wasikun na su.
Ya tabbatar wa Shugaban kasar da kudurinsu na aiki tare da gwamnatinsa don kara bunkasa da karfafa kawancen kasashen da kawancensu da Tarayyar Najeriya.