?ungiyar dake fafutukar kare ha??in bil’adama da saka ido kan al’amuran ku?i (SERAP) ta ro?i shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da Naira Biliyan 4.5 ku?in tallafin korona a Jihar Kogi.
Gwamnatin tarayya ta tura ma gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 4.5 da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don ya?i da cutar COVID-19, kamar yadda aka ake wa sauran Jihohi.
SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar inda ta ro?i shugaba Buhari da yaba Ministan shari’a da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa umarnin bincikar yadda aka ?asafta ku?in.
A jawabin SERAP ta ce: “Da zarar an sami ?wa??warar shaida, duk wanda ake zargi a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.”
A jawabin Mataimakin shugaban ?ungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu ya bayyana cewa: “Bada umarnin ga ministan shari’a da kuma sauran hukumomin ya?i da cin hanci doka ce a kundin tsarin mulkin ?asar nan.” Kuma idan shugaba Buhari ya bada wannan umarnin to yana ?ara tabbatar da bayanin da ya yi lokacin rantsar dashi.
“Zan tabbatar da duk wasu ayyuka an gudanar da su yadda ya kamata a dukkan matakan gwamnati” inji Buhari.”Kamar yadda ka fa?a a wancan lokaci, ya zama wajibi gwamnatinka ta fa?a?a ya?i da cin hanci da rashawar da take yi zuwa dukkan matakan gwamnati uku da muke da su,” cewar SERAP.
?ungiyar tace ta damu da yawan korafe-korafe kan cin hanci da rashawa da kuma amfani da ku?a?en gwamnati ta inda bai kamata ba a dukkan jihohin Najeriya.
?aukar ?wa??waran mataki na yin bincike zai ?ara tabbatar da gaskiya da ri?on amanar gwamnati wadda ta ?unshi jigar Kogi. “Zamu yi matukar jin da?i idan aka ?auki mataki akan korafin mu cikin kwanaki 14 da tura shi.
Idan kuma ba ayi komai ba bayan wannan lokacin, SERAP zata ?auki matakin da doka ta tanadar wajen ?alubalantar gwamnati har ta yi abinda ya dace.” Cewar SERAP.
SERAP ta tura cikakken bayanin da tayi a jawabinta zuwa ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami, shugaban ICPC, Professor Bolaji Owasanoye, da kuma shugaban Hukumar ya?i da cin hanci ta ?asa (EFCC) Abdulrasheed Bawa.