Shugabar wata kungiya mai rajin ganin mata sun tsaya da kafafunsu, Joe Okei-Odumakin, ta roki babban sifeton rundunar ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya kori jami’an ‘yan sandan da suka taba yi wa wata mace ciki ba tare da aure ba.
Okei-Odumakin ta bayyana hakan ne yayin martani akan korar wata ‘yar sanda, Olajide Omolola, saboda ta yi ciki ba tare da aure ba.
Yayin tattaunawar ta da jaridar Punch ranar Alhamis, ‘yar gwagwarmayar ta bayyana korar Omolola a matsayin “zallar nuna wariya da banbancin jinsi”.
A cewar ta, jami’an ‘yan sanda da dama, a baya da kuma har yanzu, sun yi wa dumbin mata ciki ba tare da aure ba. Okei-Odumakin ta bukaci rundunar ‘yan sanda ta fara girmama jami’anta Mata kamar yadda take girmama jami’ai Maza.
“Babban abin takaici ne ace a wannan zamanin rundunar ‘yan sanda ta nuna irin wannan halayya ta daukan mataki mai tsanani akan jami’ar ‘yar sanda,” a cewarta.
‘Yan Nigeria da dama sun bayyana mamaki da bacin ransu akan hukuncin da rundunar ‘yan sanda ta zartar akan Omolola saboda kawai ta yi ciki ba tare da aure ba.