Korar Ma’aikata Da El Rufa’i Ya Yi Zai Haifar Da Matsalar Tsaro – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman Mr LA ya bayyanankorar ma’aikata da gwamnatin jihar Kaduna tayi a matsayin babban barazana ga tsaron jihar.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar hare harren yan bindiga da garkuwa da mutane domin biyan kudin fansa. Kuma masana da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun bayyana rashin aikin yi a matsayin babban abinda ke jefa rayuwar matasa zuwa ga ayyukan ta’addanci.

Muna da kalubalen tsaro ciki da wajen jihar Kaduna, domin ko a makon da ya gabata an samu hare hare da dama a karamar hukumar chikun da igabi Wanda ko a halin da muke ciki akwai yaran mu da aka sace a kwalejin kimiyyar gandun daji Wanda a yanzu sun kwashe kusan wata daya kenan a hannun yan ta’adda.

Ya kamata mu gayawa junan mu gaskiya, a halin kuncin da talaka ke ciki a halin yanzu tallafi daga gwamnati yake bukata ba wai a kara jefa rayuwar sa dana iyalan sa cikin kunci ba.

Related posts

Leave a Comment