Korar Fulani: Martanin Arewa Ba Zai Yi Kyau Ba – Tofa

Sanannen Dattijo a yankin Arewa Alhaji Bashir Usman Tofa, ya yi gargadin cewa wadanda ke neman tada rikicin kabilanci a kasar su daina domin kare afkuwar babban tashin hankali da zai haifar da wargajewar Najeriya gaba ?aya.

Ana zaman dar dar ne a kasar tun bayan da aka ba makiyaya wa’adin kwanaki su fice daga yankin kudu maso yamma kan karuwar hare hare da rashin tsaro.

Sunday Igboho, wani mai kare hakkin Yarbawa ya fara tada rikicin a watan Janairu a jihar Oyo wadda ya janyo rasa rayyuka da dukiyoyi.

Sai dai an samu ?an zaman lafiya bayan da wasu masu ruwa da tsaki daga yankin kudu da arewa suka gana a karamar hukumar Ibarapa da ke jihar Oyo a lokacin da rikicin ya fara.

Amma abin mamaki Igboho ya kuma tafi jihar Ogun don cigaba da abinda ya fara a Oyo inda rahotanni suka ce an kashe mutum daya bayan rikici ya barke.

A sanarwar da ya fitar, Dattijo Bashir Tofa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan lamarin kafin ya kazanta, har ya kai ga matakin da ba za a iya magance shi ba.

“Ba zamu amince da kashe kashen al’umma musamman Fulani da ake yi ba a wasu sassan kasar. Wasu makiya Nigeria ne ke neman tarwatsa kasar.

“Mutane na fusata, idan aka fara ramuwar gayya a kan ‘yan kudu a nan arewa, zai yi wahala a magance lamarin.

Makiyan mu na gida da waje wadanda hukumomin tsaro sun san su na kokarin hada mu fada domin ganin mun kai matsayin da ba za a iya gyara ba.

Babu yankin kasar nan da ke zaune lafiya. Tofa ya yi kira ga shugaban kasa ya dauki mataki a kan lamarin kafin abubuwa su tabarbare.

Related posts

Leave a Comment