Komawa Ga Allah Ne Mafita Ga Matsalolin Najeriya – Atiku

An bayyana cewar hanya guda da ta saura wa ‘yan Najeriya wajen magance matsalolin da suke ciki shine komawa ga Allah, da gudanar da addu’o’i da niyyar Allah ya ceto kasar daga halin ha’ula’i da ta tsinci kanta a ciki.

Tsohon mataimakin shugaban ?asar Atiku Abubakar ne ya yi wannan jawabin a sakon da ya aike wa jama’ar Musulmi a lokacin shiga wata mai alfarma na Ramadan.

Atiku ya yi wannan kira ne a wani sakon tuwita da ya aike yana taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar shiga watan azumin Ramadana.

Sannan ya ja hankali kan muhimmanci amfani da wannan watan wajen neman tuba da sau?in matsalolin da suka addaabi ?asar da ci gabanta.

Ya kuma ?ara da cewa wannan lokaci ne na waiwaye da inganta kyawawan ayyukan da yawaita taimako da sadaka musamman ga ma?ukata.

Related posts

Leave a Comment