Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai karrama Shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala da lambar girmamawa ta GCON.
Okonjo-Iweala wadda tsohuwar ministar kuɗi ce a Najeriya, ta taya ‘yan ƙasar murnar cika shekara 62 da samun ‘yancin-kai, inda ta yi amfani da damar wajen gode wa Buhari da ‘yan ƙasar.
“Ina godiya ga Mai Girma Shugaban Ƙasa da ‘yan Najeriya saboda girmama ni da za a yi da lambar GCON,” a cewarta cikin wani saƙon Twitter da ta wallafa a yau Asabar.
GCON na nufin Grand Commander of the Order of the Niger a turance kuma ita ce lambar girma ta biyu mafi girma a Najeriya.
Rahotanni sun ce Buhari zai karrama mutum 437 a bikin da za a yi ranar 11 ga watan Oktoba da lambobi daban-daban, cikinsu har da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Abba Kyari, da mawaƙi Burna Boy, da Mataimakiyar Sakataren MDD Amina Mohammed.