Kisan Zabarmari: Laifin Manoman Ne – Garba Shehu

Kakakin Shugaban kasa Muhammad Buhari, Malam Garba Shehu a wani martani da yake mayarwa game da kazamin harin da aka kai kauyen Zabarmari dake karamar hukumar Jere ta Jihar Borno, Ya ce ai suma Manoman ya kamata su tabbatar da ingancin tsaron gonakin su a wajen Jami’ai kafin su shiga gonakin su.

Kazalika Malam Garba Shehu, ya kara jaddada cewar kada Al’ummar Najeriya su raina aikin Jami’an tsaro da Jagorancin Shugaban kasa Muhammad Buhari, a fannin bayar da ingancin tsaro a kasar nan, musamman a yankin Arewa maso gabashi.

Garba Shehu ya yi wannan furuci ne a yayin wata tattaunawa ta kai tsaye da Gidan Talabijin na Channel ya yi dashi dangane da mummunar ta’asar da Boko Haram ta yi na kisan Manoma 43 a kauyen Zabarmari da ke jihar Borno.

Idan kuka kula da kyau ai baa gabaki daya yankin ake fama da rashin tsaron ba, wani bangare ne kawai, kuma shima ana ta kokarin ganin an daidaita koma don tabbatar da tsaro da kare rayuwar al’umma da dukiuoyin su; inji shi

Babu wani mutun da bai shiga damuwa ba game da wannan mummunar aika aikar da aka gudanar musamman Shugaban kasa Muhammad Buhari, da yake jagorantar kasa kuma hakan na ci mishi tuwo a kwarya.

Idan baku manta ba jiya Lahadi ne aka Gwamnan Babagana Umara Zulum ya jagoranci Jana’izar Manoman Shinkafa 43 da yan kungiyar BokoHaram suka yima yankan Rago a Gona, Wanda hakan ya fusata Al’ummar Najeriya musamman daga yankin Arewaci wanda ya jawo kowa yake fadin maganganu son ran sa.

Related posts

Leave a Comment