Kisan Zabarmari: Fafaroma Ya La’anci Boko Haram

Shugaban darikar katolika na mabiya addinin Kirista, Fafaroma Francis ya fito ya soki harin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai a jihar Borno, tare da yin Allah wadai da la’antar ayyukan ?ungiyar.

Babban limamin na Rome ya soki harin ta’addancin ne a hudubar da ya saba yi a kowane mako a fadarsa dake Vatican.
“Ina so in tabbatar da addu’a ta ga Najeriya, inda cikin takaici, aka sake zubar da jini a harin ta’addanci.”

Fafaroma ya kira abin da ya auku a garin Zabarmari, jihar Borno, kisan gilla daga ‘yan Boko Haram da ke tada kayar baya.
Shugaban Katolikawan ya yi wa wadanda aka kashe addu’ar samun rahamar Ubangiji, sannan ya yi wa iyalan da su ka bari addu’a, sannan ya roka wa ‘yan ta’addan tuba.

“Mu na rokon Ubangiji ya yi masu kyakkyawar tarba cikin aminci, Ya ba danginsu dangana, Ya canza zuciyar wadanda su ke ta’adin da ke bata masa suna.”

A wannan harin, ‘yan ta’addan sun karkashe manoman ta hanyar yanka wuyayansu a cikin gonaki.

Maganar Fafaroman ta zo ne kwanaki bayan ‘yan ta’addan sun shiga har gonakin wasu Bayin Allah fiye da 40, sun yi masu yankan rago a ?auyen Zabarmari dake yankin ?aramar Hukumar Jere a jihar Borno.

Related posts

Leave a Comment