Hadakar kungiyar Matasan Arewa maso gabashin Najeriya sun fusata damn tin Allah wadai, ganin yadda yan’ta’adda suka kashe rayukan manoma 43 a kauyen Zabarmari a jihar Borno, da kuma harsashen alkalman zasu fi haka kawo Iyan yanzu.
Matasan sun shaida wa manema labarai a daren jiya laraba a lokacin da suke zantawa da yan’ jaridar kan wan nan batu na kisan gillar, da kuma kiran gwamnatin tarayya da ta tabbatar da aiwatar da shawarwarin gwamna Zulum na jihar Borno
Shugaban kungiyar Matasan Barrista Hussaini Saraki, da ya jagoranci mambobinsu yana jan hankalin gwamnatin tarayya da tayi aniyar sake sabon tsari kan yaki da yan’tada kayan baya, biyo bayan kashe kashen rayukan manoma akan hanyarsu na zuwa gona.
Kana suka ce maganan gwamnan Borno Pafesa Baba Gana Zulum ya na kan hanya, da cewa gwamnatin tarayya da ta dauki matasan jihar da kuma na yankin a aikin Soja dana Yan’sanda da ma sauran jami’an tsaro don kawo karashen wan nan bala’i da ya addabi arewacin kasan.
Hakanan, ya kara da cewa a cikin kundin shari’ar kasa da akayi ma kwaakwarima na 1999 shafi 14 sakin layi na 2 cewa gwamnatin tarayya tsaron rayukan al’umma da dukiyoyinsu shine babban abunda gwamnati zata a gaba.
Barristan ya kara da cewa duk inda aka rasa hakan toh gwamnati bata da wani amfani.
“Kisan gillar da akayi ma
Mutanen nan ya zama dole gwamnati ta sake fitar da sabon tsari don tunkarar mayakan nan, sojojin Najeriya dole su sake sabon salon yaki irin na sunkuru, tunda suma yan’tada kayan bayan suna chanza yadda suke kai hare hare da kisan mutane kaman kiyashi, gaskiya abun ya ishe mu haka”. Ya jadadda.
“Shuwagabanin mu na arewa sunyi shiru suna kallo, Arewacin Najeriya gaba naya muna cikin Jimamin abun da ya faro, a yayin da ake ci gaba da neman wadan da suka bata a cikin jeji haryanzu babu labarinsu”.
Shugaba kungiyar ya kar kare da cewa su ba suna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka bane, ko yayi awon gaba da hafsoshin soji ya kawo wasu ba, a a munasu akawo chanji na sabon tsarin yaki da yan’tada kayar bayanne, a cewarsa amma idan hakan bai samu ba zasu yanke ma kansu matsaya, ko ta ware ko ta waraye.
Daga Adamu Shehu Bauchi