Kisan ‘Yan Arewa: Babu Batun Yin Ramuwa – Gwamnonin Arewa

Kungiyar gwamnonin Arewa sun bukaci mutanen arewacin Najeriya da kar su dauki fansa kan ‘yan kudu da ke zaune a kowane yanki na arewa saboda rikicin kabilanci da ake fuskanta a wasu sassan jihar Oyo.

Kungiyar ta lura cewa irin wannan matakin ba zai magance matsalar da kasar ke fuskanta ba a yanzu, amma zai kara fadada ta.

Sai dai kuma, kungiyar ta gwamnonin Arewa ta ba mutanen Arewa tabbacin cewa tana yin duk abunda ya dace don magance matsalar da ta shafi wasu ‘yan arewa a jihar Oyo.

Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato wanda shi ne shugaban kungiyar ya yi wannan rokon yayin ganawa tsakanin kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da NSGF a masaukin gwamnan Filato da ke Abuja.

“Wannan taron ya zama dole kuma ya zama wani bangare na tattaunawarmu tun lokacin da batun barazanar wa’adin barin gari ya fara daga kungiyoyi daban-daban a kasar.

“Mun tattauna da shugabanni daga arewa don nemo mafita da kwantar da tashin hankalin da ke faruwa a yanzu sakamakon rikicin da ya barke a jihar Oyo.

“Babu wata fa’ida a daukar fansa kan ‘yan kudu da ke zaune a arewa. Mun tura wakilai zuwa Oyo don sanin halin da ake ciki da gaskiyar abin da ya faru.

“Da yardar Allah za mu kai ga tushen matsalar. Kasar ta dukkanin mu ce. Ba ma so mutane su ce wasu su bar yankin. Wannan sam sam ba za a yarda da shi ba.”

Related posts

Leave a Comment