Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kisan Soji A Kaduna: Labarin Bai Cika Ba – Lai Mohammed

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Yaɗa Labarai a Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da kai hari kan sansanin sojan ƙasar da ‘yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.

Ministan ya ce duk da cewa kafofin yaɗa labarai da dama sun ruwaito harin amma sun gaza wajen ruwaito yadda sojojin Najeriya suka fatattaki maharan.

Sojoji aƙalla 11 rahotanni suka ruwaito an kashe a harin na ranar Lahadi lokacin da maharan suka far wa sansanin nasu da ke yankin Birnin Gwari.

Kazalika, an ƙona motocin soja masu sulke uku.

“Tabbas an kai hari kan sansanin soja a Kaduna amma abin da ‘yan jarida ba su rawaito ba shi ne yadda aka daƙile harin da kuma ɓarnar da aka yi wa ‘yan ta’addan,” in ji ministan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa a jiya Laraba.

Sai dai ministan bai bayyana adadin sojojin da aka kashe ba.

Exit mobile version