Wata tawaga ta gwamnatin tarayya bisa ga umarnin mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari karkashin jagorancin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, sun isa garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.
Tawagar sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya ne a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma 43 a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere ta jihar.
An tattaro cewa manyan jami’an gwamnatun sun isa garin Maiduguri a ranar yau Litinin, 30 ga watan Nuwamba, domin sauke nauyin gabatar da ta’aziyar ga ‘yan uwan mamatan da kuma jihar Borno gaba ɗaya.
Sanarwar ziyarar tasu na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da hadimin Shugaban majalisar dattawan akan yaɗa labaraiOla Awoniyi ya fitar a yau Litinin, 30 ga watan Nuwamba.
A cewar sanarwar, waɗanda ke cikin tawagar sun hada da Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da ministan birnin tarayya, Mohammed Bello, da ministan sadarwa, Ali Pantami. Sauran sun hada da mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno (mai ritaya), karamin ministan noma, Mustapha Baba Shehuri da kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu.
An ruwaito cewa tawagar sun samu tarba a filin jirgin sama daga mataimakin gwamnan jihar Borno, Usman Umar Gadafu. Tawagar sun ziyarci Borno a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya domin yin ta’aziyya ga iyalan mamatan, gwamnati da kuma mutanen Borno kan mummunan al’amarin.