Rundunar sojin kasa ta ce ba za ta gabatar da sunayen jami’anta da aka tura Lekki Toll Gate ba, a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, wa?anda ake zargi da kisan masu Zanga-Zangar Endsars.
Faruwar al’amarin ya janyo hankalin mutanen ciki da wajen Najeriya, yayin da aka zargi sojoji da gwamnatin tarayya da tozarta hakkin bil’adama, ta hanyar bu?e wuta ga Matasa masu Zanga-Zanga.
Duk da rahotanni na nuna an kashe mutane da dama, amma har yanzu kisan mutum daya kacal aka tabbatar.
A wata tattaunawa da aka yi da Kakakin Rundunar Soji ta 81 Osoba Olaniyi, yace Sojojin da suka yi aiki a ranar basu amsa sunansu ba.
“Hakan ya ci karo da yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu. A yadda mutane suka yi ta bayar da labarai, kamar muna yakar ‘yan ?asa ne, wanda hakan kuskure ne,”.
Dama rundunar sojojin ta musanta faruwar lamarin. A wata sanarwa da rundunar sojoji suka yi a shafinsu na Twitter, sun ce labarin bude wutar da aka ce sojoji sun yi a toll gate karya ne.
Amma a makon da ya gabata, Olaniyi ya tabbatar da cewa sojoji suka yi wannan aikin. Ya ce gwamnatin jihar Legas ce ta nemi sojoji da su tabbatar da samar da zaman lafiya bayan rikicin da ya barke.
Daga faruwar zanga-zangar EndSARS, babu wani soja da ke karkashin runduna ta 81 da ke jihar Legas da yayi wannan aika-aika,” kamar yadda ya shaida a takardar.