Kisan Lekki: An Yi Karar Buhari Da Buratai Gaban Kuliya

Wani ƙwararren Lauya mai zaman kanshi mai suna Barista Olukoya Ogungbeje, ya gabatar da karar biyan diyyar Naira biliyan 10 a kotu, ya na kalubalantar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Lauya Olukoya Ogungbeje ya kuma hada shugaban hafsun sojin kasa, Janar Tukur Buratai da wasu mutane a wannan shari’a a kan harbe ‘yan zanga-zangar #EndSARS da aka yi a Lekki Jihar Legas.

Lauyan ya na ikirarin jami’an tsaro sun bude wa Bayin Allah masu zanga-zangar lumanar #EndSARS wuta a Lekki, a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2020 bisa ga zalunci da cutarwa bisa ga umarnin Shugaban ƙasa da Shugaban dakarun Sojin ƙasa.

A wannan shari’a wadda za ayi a gaban kotun tarayya ta Legas, Barista Ogungbeje ya roki Alkali ya bayyana harbe-harben da aka yi a matsayin abin da ya saba doka, kuma ya keta hakkin bil’adama da nuna tsagawaron rashin imani daga ɓangaren jami’an tsaro.

Lauya Ogungbeje ya na ikirarin harbe masu zanga-zanga ya ci karo da dokar kasa, haramun ne, kuma zalunci ne da wuce gona da iri a tsarin mulkin farar hula, wanda ya kamata Kotu ta ɗauki matakin Shari’a cikin gaggawa.

Rokon da Lauyan ya ke yi a gaban kuliya shi ne a biya wadanda aka yi wa harbin kisan gilla na babu gaira babu dalili Naira biliyan 10 domin su rage zafi. “Amfani da karfi da harbin ‘yan zanga-zangar lumuna keta hakinsu ne na rayuwa, domin doka ta bada damar a sauraresu da shirya taro kamar yadda tsarin mulki ya tanada.”

Lauyan ya ce abin da jami’an tsaro su ka yi ya saba wa sassa 33, 36, 38, 39 da 40 na tsarin mulki. Sauran wadanda ake kara su ne Sufetan ‘yan sanda, hukumar ‘yan sanda, SSS, darektan SSS, gwamnatin Legas da kwamishinan shari’ar ta da kuma AGF.

Labarai Makamanta

Leave a Reply