Kisan Fulani A Nasarawa: Miyyeti Allah Ta Yi Tir Da Rashin Maganar Buhari

Kungiyar kare hakkin makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN ta bayyana takaicinta game da shirun gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari kan harin Bam din da ya hallaka Fulani Makiyaya 40 a jihar Nasarawa.

Kakakin kungiyar Miyetti Allah, Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa wannan kisan gilla da aka yiwa al’ummarsu abin tir ne kuma wajibi a gudanar da bincike kan yadda Bam ya tashi da fulanin.

A jawabin da yayi, yace: “Ko ba komai, ya kamata Shugaban kasa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan ta’addanci.”

“Abin kunya ne cewa yayinda aka kashe mutane, shugaban kasa na can jihar Katsina na shan walima.”

“Muna kira ga hukumar kare hakkin dan adam ta gudanar da bincike kan wannan lamari da kuma kashe-kashen da Sojin sama ke yi a Nasarawa.” “Wadannan makiyayan da aka kashe yan Najeriya ne, suna da hakki kaman ko wane dan Najeriya saboda haka wajibi ne doka ta kare su.”

Gwamnan Nasarawa ya bayyana An yi jana’izar Fulani Makiyaya 37 da Bam ya hallaka a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa. Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana hakan a jawabin da yayi a shirin ‘Politics Today’ na tashar ChannelsTV da yammacin Alhamis.

“Mun birne mutum 37 jiya, ina da wannan tabbaci. Takwara na jihar Benue ya ce suma sun birne mutane a jiharsu.” “Mutum tara cikin yan gida daya ne. Fulanin jihar Nasarawa, kuma mahaifinsu ya zo na yi masa ta’aziyya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply