Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, ya ba Gwamnati Shawarar cewa kamata yayi a kashe gaba dayan ‘yan Bindiga.
Ya bayyana hakane a wajan taro na musamman da aka yi a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamna El-Rufai yace ta hakane kawai za’a samu zaman Lafiya a makarantu da sauransu.
Yace duk wani dake zaune a cikin daji yana da Laifi dan haka kawai ya kamata Sojojin sama dake da kayan aiki suwa dazukan Najeriya da masu laifi ke boye a ciki luguden wuta.