Kisa Ne Maganin ‘Yan Bindiga Ba Sulhu Ba – El Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya sake jaddada matsayarsa kan cece kucen da ake yi na yin afuwa ga ‘yan Bindiga inda ya ce masu wannan tunani suna da karancin hangen nesa babu wata hikima ko tasiri na yin sulhu da ‘yan Bindiga.
“Mu kashe su kawai, idan ya so wa?anda suka rage sai mu duba yiwuwar kar?ar tubansu”.

El-Rufai ya yi wa?annan batutuwa ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar ranar Juma’a, 19 ga Fabarairun 20121 kan makomar Najeriya mai taken The Fierce Urgency of Now: Tactics and Strategies to Pull Nigeria from the Brink, wanda aka gudanar a Jihar Legas.

An sha jin gwamnan wanda ya ta?a jagorantar wani kwamitin jam’iyyarsu ta APC kan sake fasalin Najeriya, yana bayyana cewa ya kamata a sake duba fasalin ?asar domin ?ara wa jihohi ?arfin iko.

A jawabin nasa na ranar Juma’a, El-Rufai ya ce ‘yan sandan Gwamnatin Tarayya ba za su isa ba.

“Abu ne mai mahimmanci a samar da tsarin tsaro na tarayya da na jiha da na cikin al’umma. ba mu da isassun ‘yan sanda. ‘Yan sandan Gwamnatin Tarayya ka?ai sun yi ka?an,” a cewarsa.

Wani abu da gwamnan ya ta?o shi ne maganar kashe-kashen da ‘yan bindiga ke aikatawa a kowace rana, abin da ya bayyana da cewa Najeriya “na rasa ?arfin ikon da take da shi a matsayinta na ?asa”.

A cewarsa: “Najeriya a matsayinta na ?asa ta gaza kare muradunta da kimarta a matsayinta na mai samar da tsaro da kare ha??i da kuma tabbatar da doka.

“Wannan ne dalilin da ya sa ‘yan bindiga ke kawo mata wargi duk da ?arfin ikonta kuma ta hanya mafi muni da tsoratarwa.”

Kazalika, El-Rufai ya ce akwai bu?atar a sauya tsarin shari’a a Najeriya, ta yadda za a bai wa kotunan Jihohi ?arfin ikon gudanar da wasu shari’o’i.

“Abin da nake bayar da shawara a nan shi ne, a rage wa tsarin shari’a a matakin tarayya ?arfi nan take, ba gobe ba, ba anjima ba.

“Tsarin shari’ar da ake bi yanzu yana yin jinkirin da ke kawo tsaiko wurin maganin matsalolinmu, har ma ‘yan ?asa su ri?a tunanin tuni har an saki masu laifin ma, kuma hakan ?arfafa wa masu niyyar aikata laifi gwiwa.”

‘A bai wa jihohi ikon mallakar arzi?insu’

Gwamnan ya ?ara da cewa tun da dai jihohi ne ke da ikon mallakar filaye ko ?asar da ke garuruwansu, to ya kamata su mallaki arzikin da ake samu daga ma’adanan da ke ?asashen nasu – amma su biya haraji ga Gwamnatin Tarayya.

“Dole ne mu gyara kundin tsarin mulki domin tabbatar da mallakar man fetur da iskar gas da ma’adanai da ke jihohi, wa?anda da ma su ne ke da iko kan ?asa bisa dokar ?asa.”Su kuma sai su biya Gwamnatin Tarayya haraji.”‘A rage kashe ku?i wurin tafiyar da gwamnati’.


Kafin gwamnan ya ?are jawabinsa sai da ya bayar da wasu shawarwari da yake ganin su ne mafita ga ?orewar Najeriya, ciki har da rage ku?in tafiyar da gwamnati da ?ara azama wurin kar?ar haraji da mutunta ha??in kowane ?an ?asa da sayen makamai ga jami’an tsaro.

“A yi gagarumin yun?uri wurin rage ku?in tafiyar da gwamnati a matakin tarayya da ?aramar hukuma ta hanyar ha?e ma’aikatun da ke da aiki iri ?aya, sannan kuma a jingine batun ?ir?irar wasu gwamnatoci ko hukumomi saboda gaba.”

Related posts

Leave a Comment