Kisa Ga Wanda Ya Zagi Annabi: Lauya Falana Ya Yi Karar Buhari Da Ganduje

Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam kuma babban lauyan Najeriya, Femi Falana, ya mika korafi ga hukumar kare hakkin dan Adam da ke Banjul, kasar Gambia, a kan hukuncin kisa da aka yanke wa mawakin Kano.

Falana ya bukaci hukumar da ta yi amfani da karfin isarta kamar yadda dokokin hukumar ta bayyana na 2020.

Falana a korafinsa mai kwanan wata 8 ga Satumban 2020, ya ce: “Ina korafi a madadin Sharif Yahya Sharif inda nake bukatar hukumar da ta duba matakanta.

“Wannan bukatar mun miko ta a madadin Sharif Yahya Sahif wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamkaon batanci da yayi a jihar Kano da ke Najeriya.”

Idan za ku tuna mun ruwaito muku cewa, majalisar limaman masallatan Juma’a na jihar Kano, sun jinjinawa hukuncin da aka yanke wa matashin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad.

An yankewa matashi Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa ne a wata kotu da ke jihar Kano a kan wakar batanci da ya yi ga Annabi Muhammad S.A.W.

Shugaban majalisar, Muhammad Nasir Adam, kamar yadda Kano Focus ta ruwaito, ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar da ya sa hannu a kan takardar.

Sharif-Aminu, mazaunin kwatas din Sharifai da ke birnin Kano, an maka shi gaban kotu ne sakamakon batanci da ya yi ga Annabi, wanda hakan ya ci karo da sashi na 382, sakin layi na 6 na dokokin shari’ar Musulunci na jihar Kano.

Mawakin ya yi kalaman batancin ne cikin waka wacce ya watsa ta a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp a watan Maris na 2020.

Labarai Makamanta