KIRSIMETI: Mailantarki Ya Yi Wa Kiristocin Gombe Watandar Buhunan Shinkafa, Man Girki Da Kudin Cefane

Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmad Mailantarki, ya yi wa Kiristocin Jihar Gombe watandar kayan abinci domin sauƙaƙa masu wadatar abinci a lokacin Kirsimeti.

Kayayyakin abincin waɗanda aka raba kwana ɗaya kafin ranar Kirsimeti, sun haɗa da shinkafa, man girki da kuma tallafin kuɗaɗe.

An raba kayan ga coci-coci, Kungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) reshen Jihar Bauchi da sauran ƙungiyoyin Kiristoci na cikin jihar.

Da ya ke rabon kayan abincin a ranar Asabar a Gombe, Mailantarki ya ce wannan ƙoƙari da ya yi, ya yi ne domin ya sauƙaƙa masu gudanar da Kirsimeti ba cikin halin damuwa ba.

Daga nan ya roƙe da su yi koyi da Annabi Isa (AS). Ya ƙara da cewa lokacin Kirsimeti, lokaci ne da jama’a za su ƙara himma wajen ƙara kusantuwa da Ubangiji, tare da fatan su ga ƙasar nan ta wanzu cikin yanayin da jama’ar ta za su yi rayuwa mai kyakkyawan tasiri.

Sannan ya roƙi Kiristoci su yi koyi da Annabi Isa (AS) wajen nuna ƙauna, haɗin kan al’umma da kyakkyawar mu’amalar zamantakewa.

Mailantarki ya ce abu ne da kowa ya sani cewa babu ƙasar da za ta iya ci gaba har ta bunƙasa, ba tare da an zauna lafiya da juna ba, cikin kyakkwar zamantakewa

Daga nan ya roƙi ‘yan Jihar Gombe su fito su yi tururuwar zaɓen shugabanni nagari.

Ya ce idan aka zabe shi, ya sha alwashin bunkasa jihar sosai fiye da yadda ya ke a yanzu, nesa ba kusa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply