Kirsimeti: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Kiristoci Su Sa Najeriya Cikin Addu’o’i

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta taya Kiristocin kasar murnar zagayowar ranar Bikin Kirsimeti, tare da yin kira a garesu da suyi amfani da wannan lokacin wajen sanya Najeriya cikin addu’o’i na ganin ƙarshen matsalolin tsaro dake addabar kasar.

Ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya yi wannan kiran a sakon bikin zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti da ma’aikatar tsaro ta kasa ta fitar domin taya Kiristocin kasar murna da wannan muhimmiyar rana.

Ya bukaci Kiristocin da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa ‘yan uwansu ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

Ministan tsaron ya bayyana bukatar zaman lafiya tsakanin mutane, hadin kai da kuma lumana musamman irin wannan lokacin da kasar ke yaki da ayyukan tada kayar baya, ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane da ma wasu munanan ayyuka.
Ya ce akwai bukatar a koma ga Allah ta hanyar addu’o’i don tallafawa jami’ai wajen yakar ayyukan bata gari.

Da yake jinjinawa jami’an sojoji – wanda sakamakon aikin su, wanda aikin su shine tsare rayukan yan kasa, ba zasu su samu damar zuwa yin shagulgulan Kirsimeti cikin iyalan su ba – ya tabbatar musu cewa babban kwamandan jami’an tsaron Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ba zai bar sadaukarwarsu ta tafi a banza.

Janar Magashi ya bayyana cewa hanyar da za a bi don nuna godiya ga jami’an tsaro da suke aiki ba dare ba rana don ganin ‘yan Najeriya sun yi bacci mai dadi (wanda su basa yi) shi ne ayi musu addu’a kuma a dinga sanya idanu a irin wannan lokaci na rashin tsaro.

Ya godewa jagorancin hukumomin tsaro da kuma manyan hafsoshin tsaro da raguwar jami’ai dama sauran mutane a yunkurin da su kayi kwanan nan wajen cetowa tare da dawo da daliban Kankara, Jihar Katsina.

Ministan ya bayyana nasarar da aka samu wajen ceto yaran a matsayin dakile ayyukan masu garkuwar, ya ce nasarar ita ce babbar kyautar Kirsimeti da karshen shekara ga kasar nan.

Ministan ya umarci jami’an da ke wurare daban daban da su mayar da hankali wajen tsaurara tsaro a fadin kasar; ya kara da cewa jami’an zasu tabbatar da an gudanar da shagulgulan karshen shekara lafiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply